Akwai ‘yan ta’adda da yawa a Kiristocin Najeriya bayan Nathaniel Samuel – Lauretta Onochie
A r anar Talata ne mataimakiyar shugaban kasa ta musamman a fannin watsa labarai, Lauretta Onechie ta tabbatar da cewa Nathatiel Samuel da aka kama a lokacin da yake kokarin tashin bam a cocin nan ta Living Faith ba shi kadai bane dan ta’adda Kirista a Najeria. Onochie ta bayyana cewa Samuel tsohon Malamin coci ne, amma yayi kokarin dasa bam a cocin Living Faith dake Kaduna, amma bai samu nasara ba saboda kamashi da jami’an tsaro sukayi. Nathaniel wanda aka kama a ranar Lahadi a lokacin da yake kokarin sanya bam din ya bayyana cewa yana bin addinin Kiristanci ne sannan yana halartar makarantar Living Faith Bible domin ya zamo Malamin coci. A daya bangaren kuma tsohon ministan jiragen sama, Femi Fani Kayode, ya bayyana cewa wanda aka kama din Musulmi ne ba Kirista bane. Amma a lokacin da masu daukar labarai suke tambayar wanda aka kama din a hukumar ‘yan sanda ta jihar Kaduna a jiya ya bayyana cewa sunan sa Nathaniel ba Muhammed Nasiru Sani ba kamar yanda ake yayatawa. A cik