Akwai ‘yan ta’adda da yawa a Kiristocin Najeriya bayan Nathaniel Samuel – Lauretta Onochie

A ranar Talata ne mataimakiyar shugaban kasa ta musamman a fannin watsa labarai, Lauretta Onechie ta tabbatar da cewa Nathatiel Samuel da aka kama a lokacin da yake kokarin tashin bam a cocin nan ta Living Faith ba shi kadai bane dan ta’adda Kirista a Najeria.
Onochie ta bayyana cewa Samuel tsohon Malamin coci ne, amma yayi kokarin dasa bam a cocin Living Faith dake Kaduna, amma bai samu nasara ba saboda kamashi da jami’an tsaro sukayi.
Nathaniel wanda aka kama a ranar Lahadi a lokacin da yake kokarin sanya bam din ya bayyana cewa yana bin addinin Kiristanci ne sannan yana halartar makarantar Living Faith Bible domin ya zamo Malamin coci.
A daya bangaren kuma tsohon ministan jiragen sama, Femi Fani Kayode, ya bayyana cewa wanda aka kama din Musulmi ne ba Kirista bane.
Amma a lokacin da masu daukar labarai suke tambayar wanda aka kama din a hukumar ‘yan sanda ta jihar Kaduna a jiya ya bayyana cewa sunan sa Nathaniel ba Muhammed Nasiru Sani ba kamar yanda ake yayatawa.
A cikin wani rahoto na Onochie ta kara da cewa wannan abu daya faru yana daga cikin shirin su na kokarin raba Najeriya biyu tsakanin Kudu da Arewa.
Sannan kuma kokarin tayar da bam da akayi a cocin Bishop David Oydepos shima kokari ne na raba kan Kiristoci da Musulmai a Najeriya.
Daga Jaridarhausa.com

Comments

Popular posts from this blog

What happened in Al-Qalam University was pure love to Sheik Ismail Mufti Menk not a disgrace as reported. -Hassan Kabir Yar'adua

Rwanda launches electric bikes after grabbing headlines with homemade mobile phones